Wq/ha/Balaraba Ramat Yakubu

< Wq‎ | ha
Wq > ha > Balaraba Ramat Yakubu

Balaraba Ramat Yakubu kwarariyar marubuciyar littafan Hausa ne da ake wa lakabi littattafan soyayya. An haife ta a cikin birnin Kano a a shekarar 1959[1] . Tana daga kalilan marubuta da aka fassara littafinta zuwa harshen Turanci. Rubuce - rubucenta sun fi bada muhimmanci akan zamantakewar aure da kuma gwagwarmayar mata a rayuwar Hausawa, musamman tauye hakkin mata da mazan Hausawa kan yi, zamu ga haka a littattafan ta kamar Budurwar zuciya da mashahurin littafin ta Alhaki kuikuyo ne.

AzanciEdit

  • Talla masifa ce ga mata.
    • [1] Balaraba ta zanta haka a hirar ta da jaridar Aminiya.
  • Mu musulmai ne kuma muna da dokokin addinin mu na Musulunci a kan sha'anin aure. Amma a wasu lokuta al'adun mu suna maye gurbin addinin kuma al'adu da addini ba ɗaya bane. Ina yaki saboda ina so na nuna cewa addini da al'adu ba na da bambanci.
  • We are Muslims and we have rules in Islam for marriage and so on. But sometimes, our culture dominates the religious dictates and culture and religion are different. So, I fight because I want to stress that culture and religion are different. Probably that is why I'm called a controversial writer.
  • ...Ina taɓa maudu'in da wasu marubuta suke tsoron yin rubutu a kan su. A baya, wasu dattawa kamar tsararrakin mahaifiyata suna tunanin cewa mijin su shine na biyu bayan Ubangijin su amma sai na wayar da su cewa mijin su kamar tsaran su ne.

ManazartaEdit

  1. Femke van Zeijl, "From illiterate child bride to famous Nigerian novelist", Al Jazeera (Features), 8 March 2016.