Wy/ha/Kano

< Wy‎ | ha
Wy > ha > Kano

Kano Shi ne birni mafi girma a Arewacin Najeriya. Birnin yana a jihar Kano Najeriya.

Ganewa edit

Kano shine birni mafi girma a Arewacin Najeriya, mafi yawan mutanen Kano Musulmai ne sai ƴan ƙalilan mabiya addinin kiristanci da kuma masu bin addinin gargajiya na Bori wanda shi ne ainahin addinin Kanawa kafin zuwan Musulunci ƙasar Hausa. Hausa shi ne yaren mutanen Kano kuma shi ne yare mafi girma da aka fi amfani da shi a Kano sai Larabci mai biye masa da kuma Turanci.

Jirgi edit

Filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano shi ne filin jirgin sama na farko a Najeriya, kuma shi ne filin sauka da tashi na jiragen sama a Kano.