Muhammad Ali (an haife shi,Cassius Marcellus Clay Jr., 17 Janairun shekarar 1942 - 3 Yuni 2016) ƙwararren ɗan dambe ne, ɗan fafutuka, mai nishadantarwa kuma mai taimakon jama'a, wanda ya kasance zakaran ajin masu nauyi na duniya sau uku tsakanin shekarata 1964 zuwa 1979. An yi masa laƙabi, da Mafi Girma, ya ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin manya-manyan mutane da aka yi murna a karni na 20 kuma a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yan dambe a tarihi.