’Hauwa Maina'’' yar wasan Kannywood ce kuma furodusa wadda ta fito a cikin fim din Sarauniyar Zazzau. Ta rasu ne sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba a asibitin Kano a ranar 2 ga Mayu, 2018.
ZantuttukaEdit
- Akwai banbanci tsakanin yin wasan kwaikwayo a Nollywood da Kannywood. A Kannywood kullum muna tabbatar da cewa ba mu aikata abin da zai saba wa addininmu ko al’adunmu ba, amma a Nollywood suna sumbata, runguma, da yin duk wani abu na batsa. Wasu daga cikin ayyukansu suna iya yin fina-finan manya cikin sauƙi.
- Amma duk da haka ina son a tuna ni da Hauwa Maina 'yar Biu wadda aka haifa a Kaduna a matsayin musulma kuma na bauta wa Allah a iyakar sanina kuma ina fatan shiga aljanna a duk lokacin da na amsa kiran magabata na.