Wq/ha/Shiek Shah Alam

< Wq | ha
Wq > ha > Shiek Shah Alam

Sheikh Shah Alam ɗan siyasan Indiya ne. A cikin 2001 da 2011 an zabe shi a matsayin dan majalisa na Goalpara West Vidhan Sabha Constituency a majalisar dokokin Assam. Ya kasance dan siyasa All India United Democratic Front. Ya shiga Asom Gana Parishad a ranar 5 ga Yuli 2019.

Zantuka

edit

Kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida da na yankin suka ruwaito, Alom ya ce, “Musulmai sun mulki kasar daga shekarar 1199 zuwa 1897, amma ba su aikata wani zalunci ga mabiya addinin Hindu ba a lokacin. Sai dai kuma an yi wa musulmi wariya tun shekaru 70 da suka gabata kuma akwai wani makirci ga musulmi. Duk da haka, Musulmai sun fi yawa a Assam yanzu. Idan abubuwa suka cigaba a haka, Musulmi zasu kai hari... kawai dai suna bukatar wani lokaci.” Ya kara da cewa, "Amma mu (Musulmi) ba zamu koma Bangladesh ba, mun gwammace mu koma China ko Burma".....