Rachel Louise Carson (27 Mayu 1907 – 14 Afurelu 1964) ta kasance masaniyar ilimin halittun rayuwa ce ‘yar Amurka, marubuciya kuma mai aƙidar mazan jiya, wanda littafin ta mai tasiri Silent Spring (1962) da wasu rubuce-rubucen ta ake jinjina musu da bunkasa kungiyoyin zamantakewa ta duniya. Ana amfanuwa da ayyukan Carson a yau, musamman yadda ilimin abubuwan da ɓata muhalli ke kara bunkasa.
Zantuka
edit- Manufar kimiyya itace bincikowa da haska gaskiya. Kuma haka nike dauka gaskiyar adabi, ko da kuwa tarihin rayuwa ne ko tarihi ko almara. Ina gani, a lokacin, cewa ba zai yiwu a samu wani ɓangare daban na adabin kimiyya ba.
- Jawabin amsar Lambar yabo na Littafi na Ƙasa wanda ba na Alamara ba (1952) don The Sea Around Us; kuma a cikin Lost Woods: The Discovered Writing of Rachel Carson (1999) edited by Linda Lear, p. 91
- Iska, da teku da motsin igiyar ruwa su abubuwa ne yadda suke. Idan akwai kyawu da abun sha’awa da ƙasaita a tattare da su, kimiyya zata binciko wadannan nau’in. Idan akwai wake a littattafai na game da teku, ba wai don na saka shi bane cikin sani, sai dai babu wanda zai yi rubutu da gaskiya game da teku sannan ya cire waka a ciki.
- Jawabin amsar Lambar yabo na Littafi na Kasa wanda ba na Alamara ba (1952) don The Sea Around Us; kuma a cikin Lost Woods: The Discovered Writing of Rachel Carson (1999) edited by Linda Lear, p. 91
- Mun fara kallon mutum farko da girman kan sa da kuma hadamar sa da kuma matsalolinsa na kwana daya ko na shekara; sannan kuma daga nan kawai; kuma daga ra’ayoyinsa na son kai, muka kalla duniyar da ya wanzu a ciki, da kuma duniyar taurari wanda wannan duniyar namu ‘yar ƙanƙanuwa ce a cikin ta. Duk da haka, wannan su ne manyan gaskiya, kuma akasin su mukan ga matsalolinmu na ‘yan Adam a wata mahanga na daban. Watakila idan muka maido abun hange baya kuma muka kalli mutum ta karkashin wadannan matsaloli, ya kamata mu samu karancin lokaci da iko na halakar da kawunan mu.
- Jawabin amsar Lambar yabo na Littafi na Ƙasa wanda ba na Alamara ba (1952) don The Sea Around Us; kuma a cikin Lost Woods: The Discovered Writing of Rachel Carson (1999) edited by Linda Lear, p. 91
- Dan Adam yayi nisa sosai a cikin duniyar da ya ƙirƙira da kan shi. Ya zaba ya kebe kan shi, a cikin biranen shi na karfe da kankare, daga duniya ta zahiri da ruwa da shukoki masu tsirowa. Yana marisa a cikin tunansa na iko, yana nesa nesa zuwa binciken abubuwan da zaku kawo halakar sa da na duniyar sa.