Ngozi Okonjo-Iweala ƙwararriyar ƙungiyar tattalin arziki ce daga Najeriya kuma ƙwararriyar ci gaban ƙasa da ƙasa. A halin yanzu tana shugabantar Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), matsayin da ta fara a ranar 1 ga watan Maris,a shekara ta 2021, wanda ya sa ta zama mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko da ta rike wannan matsayi. Kafin wannan, ta taba zama Ministar Kudi ta Najeriya sau biyu kuma ta yi aiki na ɗan lokaci a matsayin Ministar Harkokin Waje.
An san Okonjo-Iweala da irin dogon aikinta a Bankin Duniya, inda ta yi aiki na tsawon shekaru 25 har ta zama Babban Darakta. An yi mata kyakkyawan suna saboda ayyukanta na sauye-sauyen tattalin arziki, yaki da cin hanci da rashawa, da kuma gudunmawar da ta bayar wajen rage talauci da inganta dabarun ci gaba a kasashe daban-daban. Ta samu lambobin yabo da dama saboda jagorancinta a harkokin kuɗi da kasuwanci na duniya.
sa da
Zantuka
edit- Yana da mahimmanci musanya a cikin zukatanmu cewa yaƙi da cin hanci da rashawa ba kawai shugabanci na gari bane. kariyar kaine. Kuma kishin ƙasa ne.
- Hanya mafi kyawu wajen ganin an temaka wa kasashen Afrika ita ce karfafawa mata guiwa wajen shiga cikin harkokin siyasa dakasuwanci.yin hakan zai sanya ƙasashenmu na Afrika su samu ci-gaba me ɗorewa ,da kuma ƙaruwar tattalin arzikin kasashenmu.
- Zamu iya canza Najeriya ne kaɗai idan muka canza halayenmu da ɗabi'unmu wajen cin-hanci da rashawa .
- Mata suna rike da rabin nasarorin al'umma a rayuwa amma kuma har yanzu wasunmu bamu saniba.
- Bai kamata abar kowa a baya ba a harkar ci-gaba musamman talakawa ...