Michelle Alexander(Oktoba 7 ga wata, shekara ta 1967), ta kasance marubuciya, mai fafutukar ‘yancin ‘yan kasa, kuma farfesa mai ziyartar jami’ar Union Theological Seminary.
Zantuka
edit- Ina ga hakika kawai saboda wanzuwar kadan daga cikin attajiran bakake Amurkawa irin su Barrack Obama, Oprah Winfrey, da Colin Powell, da kuma Herman Cain, wanda ya samar da kawalwalniya na cigaba a wariyar launin fata duk da yake a matsayin tsari har yanzu akwai miliyoyin mutane masu kala wanda ke kulle a cikin wani yanayi na kaskanci na dundundun.