Mette Frederiksen (an haife ta 19 ga watan Nuwamba, shekara ta 1977) 'yar siyasan kasar Denmark ce, wacce take aiki a matsayin Firayim Ministan ƙasar Denmark ta 27 har zuwa yau. Tun daga ranar 27 ga watan Yuni, shekara ta 2019.
Zantuka
edit- Abunda ku (mutanen Greenland) kuka saba da shi ya munanta (mutanen Greenland wanda aka raba da iyalansu kuma aka kai su Copenhagen fiye da shekaru 70 da suka gabata a matsayin wani bangare na gwaji don ƙirƙirar wasu mutane na musamman masu magana da harshen Denmark). Babu tausayin dan Adam a ciki. Babu adalci. Kuma akwai rashin imani a ciki. Mu (gwamnatin Denmark) zamu iya ɗaukan nauyi muyi abu ɗaya da yake na adalci, daga idanu na: ina mai naku haƙuri game da abunda ya faru.
- Mette Frederiksen (a shekarar 2022) cited in "Denmark PM says sorry to Greenland Inuits taken for ‘heartless’ social experiment" on The Guardian, 10 ga watan Maris, shekara ta 2022.