- Kabilun, suna ganin mata da ido daban daban, amma basu karyata ikon feminisanci. Wata sa’in suna ganin mata a matsayin matsorata, wata sa’in a matsayin masu son zaman lafiya, wata sa’in a matsayin masu iko a kan komai masu kuma masana, amma basu taba bayyana mata a matsayin marasa zuciya, wanda suka rasa taimako, masu sauki ko kuma wadanda ake zalinta. Kuma a yayin da mata a cikin wadannan kabilu, yaruka, ko gungu ka iya zama duka wadannan abubuwan,ana bayyana kowacce mace da hardaddun halayen rayuwa, rayuwar zahiri da kuma duniyar zamantakewar da take ciki.