Wq/ha/Mata da cutar HIV/AIDS

< Wq | ha

Zantuka akan Mata da Cutar HIV/AIDS

Zantuka

edit
  • Kamar yadda muka sani, cocukan Afurka na fuskantar matsanantan matsalolin rayuwa idan aka zo maganar jima’i a cikin aure. Dangane da wani bincike na UNICEF, amare ‘yan mata a wasu kasashen Afurka na kamuwa da cutar HIV fiye da ‘yan mata masu irin shekarun su wanda ke jima’i a waje ba tare da aure ba. Hakan na faruwa ne saboda amare na kamuwa daga cutar ne daga mazajen su, wadanda sun girme su sosai kuma sun riga sun kamu da cutan tun kafin auren. A zahiri, kauracewa da kuma kiyaye ta hanyar dabi’u masu kyau ba zasu yi aiki ba. Wannan sakamakon kuma ya samo asali ne daga tarihin halayyar ciwon: fiye da kashi biyu-cikin-uku na cutar na kama tsakanin goma ‘yan mata ‘yan shekaru goma sha biyar zuwa ashirin da biyar. A wash yankunan na Afurka, mata na da mata sun fi saukin kamuwa da cutar fiye da maza da suke shekaru iri daya sau biyar zuwa shida. Wahalar da ke tattare da wannan yanayi na da wuyar ganowa. Stephen Lewis, Wakilin UN na musamman akan HIV/AIDS a Afurka, ya yi sharhi akan hakan a takaice kamar haka: “Ga wannan nau’i mai ban tsoro, dole a kara da, dangane da Afurka, cewa wannan annobar a yanzu, a takaice sannan ba’a iya maido shi baya, matsanancin barazana ne ga mata da kuma ‘yan mata. Abun da ake kira “Talaucin Mata” ya tattaru ya hadu da cutar HIV.