Wq/ha/Mata

< Wq | ha
Wq > ha > Mata

Mace (tilo), Mata (jimilla) jinsi ne wanda ke matsayin kishiyar jinsin namiji. Mata suna da muhimmanci acikin al'umma saboda ta su ne ake iya samun daman hayayyafa da tara al'umma.

Mahaifiya m(mace) na shayar da ɗanta
Mata a shekaru daban daban na rayuwa

Zantuka akan Mata

edit
  • An halicci mace daga haƙarƙarin namiji na dama ne; don ya zamo kariya a gare ta
    • Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
  • Mata, iyayen gari, idan ba ku ba gari, idan kuwa kukayi yawa gari ya baci
    • Karin maganar Hausawa
  • 'Yan kubar raina mata, mata iyayenmu ne su, suna aikin jirgi, suna aikin mota, suna gyara gida..
    • Waƙar Hausa
  • Al’amurran da suka shafi mata da kananan yara musamman dangane da tallafa masu - wanda ya hada da kariya da kuma shiga cikin al’amurra, daidaituwar damammaki na gudanar da hidindimun zamantakewa da na yau da kullum har zuwa ilimi da lafiya..
    • Prof Rukayya Ahmad Rufa’i
  • Da ace babu mata a duniya, to da duka arziƙin da ke duniya sun zamo maras ma’ana
    • Aristotle Onassis
  • A matsayi na na mace banda ƙasa tawa. A matsayi na na mace kasa ta itace duniya baki daya
    • Virginia Woolf
  • Zamanki mace ya ta'allaka ne da hali
    • Chuck Woolery
  • Faɗa muhimmin ra’ayi ne na maza; makamin mace kuwa yana cikin harshen ta
    • Hermoione Gingold
  • Mata ko da yaushe abin sha'awa ne
    • Ville Vallo
  • Adalci a tsakanin jinsi muhimmin al’amari ne ga cigaba da kuma ɗorewar zaman lafiya ga kowacce kasa
    • Kofi Anan
  • A duk lokacin da mata suka cigaba, daukakin al’umma suna samun moriyarsu kuma zamuna masu zuwa na samun ingantaccen tarbiyya
    • Kofi Anan
  • Abun alfahari ga kowacce uwa shine ta haifi ɗa nagari kuma mai nasara
    • Jane Austen
  • Ya kamata mace ta tausasa namiji a wasu lokutan amma ba ta raunata shi ba
    • Signmund Freud
  • Yana da muhimmanci mu riƙa tunawa da gwarazanmu maza da mata
    • Maya Angelon
  • Ka kasance ga nagartarta mai matuƙar kyautatawa. Kasance ga kura-kuranta kuma mai ɗauke idanu kadan
    • Mathew Prior
  • Wannan rayuwarki ce!!! ‘Ya’ya/maza/masoya duka wani shafi ne guda. A duk lokacinda mu (mata) muka kara karfi, a lokacin ne da dama suke ƙara son mu
    • Cynthia Bassinet
  • Na fara sanya hulata a matsayi na na karamar lauya, saboda yana taimaka mani wajen nuna aiki na. Kafin hakan, a duk lokacin da naje wajen wani taro, wani sai ya ce mun in kawo shayin kofi
    • Bella Abzug
  • An koya wa maza yadda zasu nema gafara dangane da ajizancinsu, su kuwa mata dangane da karfinsu
    • Lois Wyse
  • ‘Yancin mata wani canji ne na iko, iko na kai da kuma zamantakewa. Yanayi ne na yadda ake kallon duniya - jayayya ga karfin iko/matsalolin mamayewa (daga wata jinsi), kuma tabbatar da karfin iko ga mata
    • Charlotte Bunch
  • Daidaita biyan albashi ga mata (dangane da na maza) maganan adalci ne mafi sauki
    • Mary Anderson
  • Namiji yana jurewa kunci a matsayin ukubar aiki, mace na rungumarsa ne a matsayin gado na yau da kullum
    • Ba’a san wanda ya fada ba
  • Baza’a taba samun cikakken adalci ba har sai mata su kansu sun taimaka wajen tsara dokoki da kuma zaben masu hanu da shuni
    • Susan B. Anthony
  • Ko da ace an bata ko an hana ta, yana farantawa mace kawai idan ta tambaya
    • Ovid
  • Mata na son maza masu natsuwa. Saboda a tsammaninsu cewa suna saurarensu ne
    • Marcel Chard
  • Nafi amincewa da kalmar mai kula da iyali, saboda matan aure kullum tunani suke cewa akwai wata mace a can waje
    • Bella Abzug
  • Nafi gamsuwa da ilhamin mace akan na namiji
    • Stanley Baldwin
  • Adireshi na kaman takalmi na ne, yana tafiya tare da ni. Ina tsayawa ne a inda ake fada da rashin gaskiya
    • Mother Jones
  • Zan sa mata su rika daukan kansu ba a matsayin siffau ba amma a matsayin suna
    • Elizabeth Cady Stanton
  • Maza ne suka kera sarkar da aka kulle mata, ba tsarin halitta jiki ba
    • Estelle R. Ramey
  • Har yanzu muna rayuwa a duniya inda mutane da yawa, har ma da mata, sunyi imani cewa mace ta dogara ne kuma tana bukatan ta dogara da zama a gida
    • Rosalynn Sussman
  • A cikin zuciyata na san cewa mace na da dama guda biyu: ko dai ta zamo mai ‘yanci (feminist) ko kuma ta zamo baiwa
    • Gloria Steinem
  • Idan mace zata zaba a tsakanin kama wani abu a iska ko kuma tsiratar da rayuwar jariri, zata zaba ziratar da jaririn nan ba tare da kula cewa ko akwai maza a wurin ba
    • Dave Barry

Manazarta

edit
  • Kabir, Hajara Muhammad (a shekarar 2010). Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.

Mahaɗar shafukan waje

edit