Mary Cassatt (Mayu 22 ga wata, shekara ta 1844 Yuni 14 ga wata, shekara ta 1926), mai zane ce ‘yar Amurka kuma mai buga da zane. An haife ta a Pennsylvania, amma ta kwashe tsawon rayuwarta na zane a Faransa, inda ta fara abota da Edgar Degas, kuma daga bisani tayi baje koli tare da impressionists. Cassatt ta kan yi zanen hotunan rayuwar gida da kuma zamantakewa na mata, tare da mayar da hankalin akan tsananin shakuwa tsakanin uwaye da ‘ya’ya.
Zantuka
edit- sorted chronologically, by date of the quotes of Mary Cassatt
- Oh wani iri nake ji in fara aiki, yatsu na suna kaikayi sosai kuma ruwan idanu na sun kosa su sake ganin hoto mai kyau.
- An ɗauko daga Nancy Mowll Mathews, in Mary Cassatt: A Life, Villard Books, New York, a shekarar 1994, p. 76 - ISBN 978-0-394-58497-3.
- Na hakura da dakin hoto kuma na yaga hoton mahaifina, kuma ban taɓa burushi ba tsawon makonni shida, ba kuwa zan taba karawa ba har sai na ga alamun komawa Turai. Na kosa matuka in koma Turai damina mai zuwa sannan in samu aiki, amma ban yanke shawarar a ina ba.
- An ɗauko daga wasikar ta na watan Yuli, shekara ta 1871; kamar yadda aka dauko daga tarihin rayuwarta a yanar gizo a [1].
- …Mu ‘yan [ Impressionist ] zamu dauki fada mara alamun nasara kuma muna bukatar duk wasu dakarun mu.
- An dauko daga c. 1879; kamar yadda aka hakayo daga Nancy Mowll Mathews, in Mary Cassatt: A Life, Villard Books, New York, a shekarar 1994, p. 118 - ISBN 978-0-394-58497-3.
- Idan dai kai [ Vollard ] zaka iya nemo wannan hoton [‘Milliners's workshop'] wanda Edgar Degas ya zana, na san dan Amurka wanda zai biya komai saboda da shi.
- Mary Cassatt, quoted by Paris' art-dealer [Vollard] , in Degas, an Intimate Portrait, Courier Corporation,a shekarar 1927, p. 90