Mary Akpobome, ta kasance darektan Bankin Heritage Ltd na Najeriya (HBCL). Itace ta assasa Gidauniyar Purple Girl, wani kungiya da ba na gwamnati ba wanda ke da alhakin inganta rayuwar ‘ya’ya mata.
Zantuka
edit- Talauci ya zamo muhimmin abu a wajen gane ko cewa ko mace zata samu ilimi
- Rayuwa ta koya mun cewa in zama mai gaisuwa ni kai na, cewa in zama mai mutunta mutane, cewa in rika taimakon mutane saboda mutane sun taimake ni nima.
- Macen da aka tallafa mawa zata ninninka al’umma. Gidauniyar zata taimaki yara mata har zuwa matakin jami’a.
- Ilimi ga yara maza da yara mata yana da muhimmanci sosai wajen cimma nasarar su ga Najeriya da kuma duniya baki daya.