Wq/ha/Marvi Sirmed

< Wq | ha
Wq > ha > Marvi Sirmed

Marvi Sirmed (an haife ta 11 ga watan Yuni, shekara ta 1970) mai magana ce akan siyasa ‘yar ƙasar Fakistan, ‘yar jarida, kuma mai fafutukar hakkin dan-Adam.

Zantuka.

edit
  • “Jiki na, ra’ayi na”, matsala ce da ta shafa matan Fakistan da yawa a duka matakai. A yayin da aka kashe mace a sunan “daraja”, ana kai hari ga jikin ta; a yayin da aka hana wa mace damar zaɓar abokin zaman ta, ana janyo jayayya a tsakanin jikinta da ra’ayin ta; kuma a duk lokacin da mace ta fuskanci cutarwa na gida, ana kai hari ga jikinta ne. Dukkannin abubuwan da kungiyar “Aurat March“ suke ƙorafi a kai, suna da muhimmanci daidai gwargwado, amma duka sun samo asali ne daga tsananin kin mata da ya mana katutu a cikin al’ummar mu. Mata basu da iko akan jikin su, kuma shine babbar matsalan, a cikin magana ta.
    • Marvi Sirmed, Pakistani feminist.