Wq/ha/Magana Jari Ce

< Wq | ha
Wq > ha > Magana Jari Ce

Magana Jari Ce wani shahararren littafi ne na Hausa wanda Abubakar Imam ya rubuta kuma ana daukan shi matsayin littafi mafi karɓuwa da aka taɓa rubuta wa a harshen Hausa. Kuma an sanya littafin acikin jadawalin darasi na Harshen Hausa don karatun sakandare a Arewacin Najeriya.

Zantuka

edit
  • Kayi ƙoƙari ka iya bakin ka.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 4. Waziri da Fasih.
  • Kome zaka yi kai dai, ka dangana da Allah da annabinsa. Muddin ka dogara dashi, duk wani makirci na mahaluƙi ba shi baka tsoro.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 5. Waziri da Fasih.
  • Idan Allah ya taimake ka, bai kamata ka gode da alfahari ba. Abinda zaka yi, sai ka dubi wanda ya kasa ka, kai kuma ka taimake shi.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 5. Waziri da Fasih.
  • Abinda ka ga dama kayi, duk ka yi, amma banda girman kai. Shine abinda ke tauye arziƙin mutane basu sani ba,
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 5. Waziri da Fasih.
  • Banda wulaƙanta mutane. Da ai arziƙi da matsiyaci, da musulmi da kafiri, da basarake da talaka, kowa ka gani ka bashi girma gwargwadon abinda ya kamata. Amma bance ka riƙa wulaƙanta kanka ba, yadda za'a raina ka. Ka tuna nan ƙasar daga Sarki sai Ni da na haife ka.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 5. Waziri da Fasih
  • Abinda yasa nace ka ba mutane girma, domin ajiyar Allah babu inda baya yinta. Sau da yawa zaka ga mutum kim, ka girmama shi, amma in ka bi cikin halinsa sai kaga ba abin a girmama bane. Da yawa kuma zaka ga mutum yaro-yaro, ka raina shi, amma in ka bibiya halinsa sai ka same shi waliyi ne, ko kuwa shaihun malami.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 5. Waziri da Fasih
  • Aikata alkairi ga kowa, sakayyar ka tana wurin Allah.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 5. Waziri da Fasih
  • Babban mugun abu ga ɗan halas ya tasamma munafinci. Kome zakayi, kai dai tsaya kan gaskiya, in yaso in za a kashe ka ne a kashe ka. Dukkan wannan ɗaukakar da ka ga Allah ya bamu tana daga rashin munafincina ne.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce pp. 5-6. Waziri da Fasih
  • Kuma idan wata masifa ta aukar maka, kada ka kuskura ka yada girmanka wajen kwaɗayi.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 6. Waziri da Fasih
  • In kana zaune cikin mutane, kana kuwa magabaci kamar yadda nike a yanzu, sai ka riƙa lura da su. In kaga kiɗinsu ya juya, kaima kuma ka yi sauri ka sake rawa. Ba wanda ke dacewa da mutanen zamani sai mutumin zamani. Im mutum ya fito maka ta hanyar ja'iri, ka nuna masa ko Ja'iri ya san da kai. In ko ya fito maka ta hanyar mummunanci, ka nuna masa ka fi damo.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 6. Waziri da Fasih
  • Abin da ka ga duk zai cuci dan uwanka, kada kayi shi. Abinda ya faru ga marigayi Waziri, ya ishe ka misali. mugunta ba ta da alfanu.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 6. Waziri da Fasih.
  • Amma ko da nace kada kayi mugunta, amma duk da haka kowa ya taɓa ka, taɓa shi. Don mutane sun ce, ɗan halas dangin gwanda ne, ba ya jimirin zungura.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 6. Waziri da Fasih
  • Kowace masifa ta sameka, kada ka damu. Sau da yawa mutum yakan so abu, yazo ya zama sharri ne gare shi. Sau da yawa kuma yakan ƙi abu, ya zo ya zama hairan ne gare shi. Ga ɗan gajeren misali, ka ga cikin kogo aka ƙyanƙyashe ni, aka rabo ni da 'yan'uwana a ɗaure, ina kuka suna kuka, amma dubi yanzu cikin benayen da nike.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 6. Waziri da Fasih
  • Kowane abu za kayi, kai dai roƙi Allah ya baka sa'a. Ba jari ne ba fatauci, kai dai a samo sa'a.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 6. Waziri da Fasih.
  • Kowanne irin arziki kaga Allah ya nufi bawansa da shi, im baka iya cewa Allah ya sa ya yi gaba ba, kada kuwa ka ce Allah ya sa ya yi baya, balle har ka riya ka aikata wani abinda zai watsa arzikin nan nasa.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 6. Waziri da Fasih
  • Duk abinda ka sa ranka za ka yi ka yi shi, kada ka ji tsoron kome. Yi, da rashin yi, duk suna ga Allah.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 7. Waziri da Fasih
  • Ko da nace maka kada kaji tsoron kome, duk da haka in ka ga halaka a fili kada ka jefa kanka don takamar kasada. Mutane sun ce an ga kabarin mai ƙuru, amma ba'a ga na matsoraci ba. Allah na taimakon wanda ya taimaki kansa.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 7. Waziri da Fasih.
  • Ka ga yanzu mu tsuntsaye ne, ƙaddara ta kawo mu nan cikin mutane ta saka. To, kada wata rana kaji ko bayammu ka kuskura ka raina halittan nan da Allah ya yi maka, dan ganin irin ta 'yan Adam. Ka dangana da baiwar da Allah ya yi maka, da ɗawainiyar da ya aza maka, ka riƙa yin godiya gare shi bisa ga haka.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 7. Waziri da Fasih.
  • In kuma Allah ya sa na ƙara haihuwa, kai da kake babba sai ka yi ƙoƙari ka gyara zumuncinku, ko da cikinku akwai waɗanda ba uwa ɗaya ku ke ba, kada ku yarda wani ya gane cikinku.
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 7. Waziri da Fasih.
  • Ni komai na tashi yi sai inyi shi haiƙan. Don tsoron mahassada bani ragewa
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 275
  • Mun san arziki ga Allah aka samu. Don zunden mahassada baya hanawa
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 275
  • Ku maƙiya ku dena sukana ga fasaha. Allah ne ya bani ba zaku hana ba
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 275
  • Ni dai na cika da sunanka Muhamman. Da salati da sallamawa ga ma'aika. Ya Allah ka yafi saɓon da na gwabza. Ya Allah ka yafi saɓon da na gwabza. Ya Allah ka yafi saɓon da na gwabza. Kayi jinƙai gareni don rahamarka!
    • An haka yo daga Littafin: Magana Jari Ce p. 275

Tushen Labari

edit
  • Abubakar, Imam (1977). Magana Jari Ce (in Hausa) (First Edition ed.). Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Zaria. pp. 4–7.