Käthe Schmidt Kollwitz (July 8, 1867 – Afurelu 22, 1945) ta kasance mai zane ‘yar Jamus, mai kirkirar zane, kuma mai sassaka wanda ayyukanta suka nuna kayatattun halin rayuwa a farkon rabin karni na 20. Tana nuna tausayinta ga masu karamin karfi ta hanyar zanen ta, sassake-sassaken ta don tausayawa wanda talauci, yunwa da kuma yaki ya shafa.
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/3/31/Kollwitzstatue.jpg/220px-Kollwitzstatue.jpg)
Zantuka
edit- Trans. Richard and Clara Winston, ed. Hans Kollwitz, Regnery Pub.; republished by Northwestern University Press, 1988
- Na fara fuskantar wani lokaci na gama gari a rayuwata inda aikk shine farko. A yayin da duka ‘ya’ya na suka yi tafiya don hutun Ista, yana da wuya inyi wani abu face aiki. Inyi aiki, inyi bacci, in ci abinci sannan in fita ‘yar gajerar tattaki. Amma fiye da komai aiki nake yi. Amma duk da haka nakan yi mamakin ko babu albarka a wannan aikin. Ba tare da an karkatar da hankali na zuwa wani wuri ba, ina aiki kamar yadda shanu ke huda.
- Diary entry (12 January 1912)
- Zuwa karshen kashi na uku na rayuwa aiki kawai ya rage. Shine kadai yake tunzurawa, yake maido da kuzari, yake saka farin ciki ya kuma cika buri.
- Diary entry (12 January 1912)