Wq/ha/Joceline Clemencia

< Wq | ha
Wq > ha > Joceline Clemencia

Joceline Clemencia (30 ga watan Nuwamba, shekara ta 1952 zuwa 30 ga watan Mayu, shekara ta 2011), ta kasance marubuciya, masaniyar harshe, Curaçaoan, bafeminiya kuma mai fafutukar ‘yanci.

Joceline Clemencia

Zantuka

edit
  • Dole mu sauya rashin dai-daito na siyasa, zamantakewa, al’adu, yanayin addini zuwa juyin juya hali don hambarar da wannan gurbatacciyar tsarin na mulkin mallakar mutanen Dutch.
  • Na tsawon lokaci, ana ɗaukan abun banza cewa mu Dutch ne; cewa Holland zata dauki nauyin mu. A cikin jahilcinmu na rashin sani ko kuma acikin rashin saninmu na jahilci, mun mance da cewa sun kasance, a tarihance ma sun kasance, masu mulki kuma mu da ake mulki, cewa kuma iko ba ya tabbatar da kan shi; dole sai an kwace shi, idan kuwa ba da takobi ba to da zuciya. Kuma mun yashar da zuciyar. Bamu nazarci sarakunan mu yadda ya dace ba, im ba haka ba kuwa da mun san cewa an tsara mu ne don mu yi tunanin cewa ba a tsara mu ba; kuma idan muka kalli ɗayan fuskan da nisa sosai kuma muka musanta wanzuwar mulkin mallaka, zata bace da kan ta. Mun manta cewa an tsara mu ne don kada mu rika ganin mulkin mallaka a matsayin mulkin mallaka.