Hilda Dokubo,(22 ga watan Oktoba, shekara ta 1969) ta kasance jarumar fim ‘yar Najeriya, mai fafutukar hakki kuma mai wakiltar matasa, wacce ta yi aiki a matsayin mai bada shawara ta musamman ga harkokin matasa ga Peter Odili, tsohon gwamnan Ribas.
Zantuka
edit- Da na zama karuwa yanzu, amma na zamo cikin rashin hutu kuma na kalubalanci rayuwa. Rayuwar ka ba zata iya inganta ta yadda idan baka kalubalanci rayuwa ba. Ko ubangiji yana kalubalantar rayuwa.
- Wani lokacin duk lokacin da na tuna da abunda mutanen da ke zama a komiti ke kawo wa, na kan yi mamakin me ke yawo a cikin jijiyoyin su. Ruwa ko jini? Saboda suna aiki kamar mutanen da basu jin zafin abubuwan da sauran mutane ke fuskanta.