Henry Louis "Hank" Aaron (Fabrairu 5 ga wata, shekara ta 1934, a Mobile, Alabama - Janairu 22 ga wata, shekara ta 2021),wanda ake yi wa lakabi da "Hammer" ko kuma "Hammerin' Hank," ya kasance dan wasan kwallon base ball, ne dan Amerika.
Zantuka
edit- Ban taba murmushi ba idan akwai bat a hannu na, wannan lokacin ne ya kamata ka mayar da hankali. Lokacin da na shiga filin wasa, babu wani abu da yake zama mun abun dariya. Bana ji ya dace in rika tafiya ina dariya.
- Kamar yadda aka hakayo daga ranar Yuli 31 ga wata, shekara ta 1956 akan batun The Milwaukee Journal; wanda aka sake samarwa a Baseball's Greatest Quotations : An Illustrated Treasury of Baseball Quotations and Historical Lore (shekara ta 2009) daga Paul Dickson, p. 2
- Ban zo nan wurin don in karanta ba, na zo ne don in doki.
- Kamar yadda aka hakayo daga cikin "Aaron Turns Bad Pitches Into Base-Hits" daga Cleon Walfoort, a cikin The Sporting News (Yuni 26 ga wata, shekara ta 1957)
- Ni.
- A yayin da aka tambaye shi wani dan wasa ne da ya zo kakar wasa mai nagartar César Cedeño, kamar yadda aka hakayo daga "Cedeno Is No. 1 in Baseball" daga United Press Interntional, a cikin The Bonham Daily Favorite (Yuli 30 ga wata, shekara ta 1972)