Goodluck Jonathan tsohon shugaban ƙasar Najeriya ne wanda ya sauka daga mulkin kasar a shekarar 2015. An haifi Jonathan a 20 ga Nuwamba 1957 a kauyen Otueke a jihar Bayelsa. Jonathan wanda yake a matsayin lamba 1 a Najeriya na tsawon watanni 60 da kwanaki 24 tsakanin (5 Mayu 2010 - 29 Mayu 2015).

AzanciEdit
- "Yayin da jirgin ruwan (dimokuradiyya) ya kara karfi, zai iya fuskantar kalubalen tafiyarta da kuma cika alkawarin da ta yi wa 'yan kasa."
- "Iskar ƴancin da muke shaƙa a yau sakamakon sadaukarwar dubban masu fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya ne, masu fafutukar kare haƙƙin bil'adama da sauran waɗanda suka shirya a matsayin kungiyoyin farar hula."
- "Siyasa ta bata fi darajar ran bil'adama ba".
- "Duk wata al'umma ko ƙasa da ta toshe muhimman ginshiƙai na sararin dimokuradiyya ba za ta iya ci gaba cikin sauri ba."
- "Ta'addanci ba shi da lamiri kuma bai bar kowa ba.."
- "Inda babu damar mutum ɗaya ƙuri'a ɗaya, to ba za'a yi masa hukunci ba kuma babu nauyi."
- "Dimokuradiyya tafiya ce da duk al'ummar da ke da tunani na ciyar da 'yancin 'yan kasarta dole ta yi."