Golda Meir, (an haife ta ranar 3 ga watan Mayu, a shekara 1898 zuwa 8 ga watan Disamba, a shekara na 1978), ta kasance 'yar siyasar, Isra'ila, malami, kuma kibbutznikit wacce ta yi aiki, a matsayin Firayim Minista na huɗu na Isra'ila daga shekara ta 1969 zuwa shekarar 1974.
Zantuka
edit- Shin ko mata sunfi maza kirki, zan iya cewa tabbas basu kasance mafi muni ba.
- Hukuma na gubantar da duk wanda ya ɗauki iko a hannun sa
- A gaskiya zan iya cewa batun nasarar wani aiki bai shafe ni ba
- Kada ka kasance mai tawali'u...ba kai kake da girma haka ba.