Emily Brontë (30 ga watan Yuli, shekara ta 1818 zuwa 19 ga watan Disamban shekarar 848), ta kasance marubuciyar littafin Turanci kuma mawakiya, 'yar uwa ga Charlotte da Anne Brontë. Ta yi fice akan littafin ta kwara daya, Wuthering Heights. Ta rubuta littafin da sunanta a matsayin Ellis Bell...
Zantuka
editLittafin I Am the Only Being (a shekarar 1836)
- Ni kadai ne dan-Adam wanda a azaba ta
babu harshen da zai tambaya babu idanun da zasu koka
Ban taba zama sanadin bakin ciki ba
Murmushin farin ciki tun da aka haife ni
A cikin murna cikin sirri - hawaye na sirri
Wannan rayuwa mai sauya wa ta kubuce
Kamar yadda bani da aboki bayan shekaru takwas
Cikin kadaici kamar ranar da aka haife ni.