Wq/ha/Eleanor Roosevelt

< Wq | ha
Wq > ha > Eleanor Roosevelt

Eleanor Roosevelt (11 ga watan Oktoban shekarar 1884 zuwa 7, ga watan Nuwamban, shekara ta 1962),yar siyasar zamantakewa ce, matar tsohon shugaban ƙasar Amurka Franklin Delano Roosevelt.

Yana daukar jarumta wajen soyayya, amma jin raɗaɗi a dalilin soyayya wuta ce mai tsafta wanda wadanda suka yi soyayyar gaskiya ne kawai suka sani.

Zantuka

edit
 
Ka yi abunda kake gani daidai ne a cikin zuciyarka - saboda za’a rika aibanta ka ko yaya. Domin za’a yi, tir da kai ida ka yo, kuma za a yi tir da kai idan baka yi ba.
  • Oh! Ina so in sanya hannuwa na a jikin ki (rungume ki), Ina mararin rike ki kusa da ni. Zobenki matuƙar nutsuwa ne (a gareni), Na kalle shi nayi tunani, tana so na ko kuwa ba zan taba sanya shi ba.
    • A cikin wani Wasika zuwa ga Lorena Hickok, Maris 7 ga wata, shekara ta 1933
  • Ka yi abunda kake gani dai-dai ne a cikin zuciyarka - saboda za’a rika aibanta ka ko yaya. Domin za’a yi, tir da kai ida ka yo, kuma za a yi tir da kai idan baka yi ba.
    • Kamar yadda aka dauko daga cikin How to Stop Worrying and Start Living ( shekara ta 1944; shekarar 1948) daga Dale Carnegie; duk da cewa ana alakanta Rooselvet da ainihin maganan, “ayi tir da kai idan ka yi, ayi tir da kai idan ka bari”. An sanya shi a cikin alamun quotation don nuna cewa itama tana da tasiri akan maganan. Ya samo asali daga shekarar 1836 daga evangelist Lorenzo Dow.
  • Fahimta kamar unguwa ce mai hanya biyu.
    • kamar yadda aka ɗauko daga Modern Quotations for Ready Reference (a shekarar 1947) by Arthur Richmond, p. 455
  • Bai isa ba kawai ka yi magana akan kwanciyar hankalin ka, dole ne mutum yayi imani da shi. Kuma bai isa ba kawai mutum yayi imani da shi. Dole ne yayi aiki akan shi.
    • Voice of America broadcast (11 ga watan Nuwamba, shekara ta 1951)
  • Dole ne mu fuskanci gaskiya cewa ko dai zamu mutu tare, ko kuma zamu koyi yadda zamuyi rayuwa a tare, sannan indai zamuyi rayuwa tare to dole ne mu tattauna.
    • The New York Times ( shekarar 1960), kamar yadda aka hakayo daga cikin The Beacon Book of Quotations by Women ( shekarar 1992) daga Rosalie Maggio, p. 156