Elaine Lan Chao (an haife ta Maris 26 ga wata, shekara ta 1953), ‘yar kasuwa ce ‘yar Amurka kuma ‘yar siyasa. Memba ce ta Jam’iyyar Republican, Chao ta yi aiki a matsayin Sakariyar Zirga-Zirga a gwamnatin Trumph daga shekara ta 2017 zuwa shekarar 2021, kuma sakatariyar Kwadago a gwamnatin Bush daga shekara ta 2001 zuwa shekarar2009.
Zantuka
edit- Zababben shugaba ya sanar da fayyatattun kudurorin shi don kawo cigaba a kasan nan ta fuskar gine-gine, bunkasa cigaban kasuwanci da tattalin arziki, da kuma samar da ayyukan yi masu kyau a kasa. Ina matukar godiya ga zababben shugaba da karramani don yi wa kasa ta aiki a matsayin sakariyar sufuri.
- President-Elect Donald J. Trump to Nominate Elaine Chao as Secretary of the Department of Transportation (Nuwamba 29 ga wata, shekara ta 2016)
- A lokacin da nike karama, mutane da gangan suke kuskure fadin suna na. Mutanen Asiya sun yi aiki tukuru don sauya wannan al’amari don ƙarni masu zuwa. Kaman bai gane cewa ba, hakan ya fada sosai game da shi fiye da yadda zai fada game da mutanen Asiya har abada.
- An dauko daga Meridith McGraw in "The private angst over Donald Trump’s racist attacks on Elaine Chao goes public" Politico (25 ga watan Janairu, shekara ta 2023)
- Martani ga maganar wariyar launin fata daga Donald Trump