Edmonia Lewis(c. Yuli 4 ga wata, shekara ta 1844 – Satumba 17 ga wata, shekara ta 1907) mai sassaka ce ‘yar Amurka.
Zantuka
edit- Babu wani abu mafi kyawu da ya fi sakakkiyar daji. Ka kama kifi a yayin da kake jin yunwa, ka sara reshen bishiya, ka hada wuta ka gasa ta, kuma ka ci shi a filin Allah, hakan ya fi kowanne abun qawa. Ba zan tsaya tsawon sati daya cir ba a birni, idan ba don sha’awar zane na ba.
- Game da dazuka a cikin “Edmonia Lewis (Smithsonian American Art Museum).
- Wasu suna yabo na saboda ni yarinya ce mai launin fata, kuma bana son irin wannan yabo… Har na gwammace ka nuna kuskure na, saboda hakan zai koya mun wani abun.
- A kan kulawa da ta ke bukata a matsayin ta na bakar mace mai zane a cikin.“Sculptor Edmonia Lewis Shattered Gender and Race Expectations in 19th-Century America” in Smithsonian Magazine (shekarar 2019 Agusta 22 ga wata).
- Ina tsananin tausaya wa mata wadanda suka yi gwagwarmaya kuma suka sha wahala.
- Gama da sculpture “Hagar” [as quoted in “Making Art Against the Odds: The Triumph of Edmonia Lewis”] (Yale National Initiative).