Eberechi Wike (née Obuzor; an haife ta 24 ga watan Mayu, shekara ta 1972)mai shari'a ce a Kotun Koli na Jihar Rivers. Ta auri tsohon Gwamna Ezenwo Wike wanda a yanzu shine Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja kuma itace matar Gwamna a tsakanin 29 ga watan Mayun shekarar 2015 zuwa 29 ga watan Mayu, shekara ta 2023.
Zantuka
edit- A ko ina a fadin duniya akwai talauci. Saboda haka, akwai mutane wadanda suke bukatar ilimi ingantacce. Kuma a duk lokacin da muka ba mutane ilimi, muna karo haske ne a cikin al'ummar mu.
- Mata sune kashin bayan kowanne iyali. Saboda haka, mune tushen kowacce al'umma. Idan munyi daidai a matakin iyali, abubuwa zasu daidaita a matakin al'umma. Idan jama'a suna cikin matsala, to hakika matsalar ta fara ne daga matakin iyali. Idan munyi daidai a matakin iyali, komai yana daidaituwa a tsakanin al'umma. Sako na zuwa ga mata shine su rika tallafawa mazajen su da kowanne daya daga cikin iyalin su.