Dean Gooderham Acheson,(an haife shi a ranar 11 ga watan Afrilu shekara ta 1893, zuwa 12 ga watan Oktoba shekara ta 1971),ya kasance sakataren kasar Amurka, a lokacin mulkin shugaban kasa Harry S. Truman. Yayi fice a wajen bada gudummawa wajen rubuta Truman Doctrine, kuma yayi fice dangane da ra’ayinsa na adawar, kwamisanci.
Zantuka
edit- Abu na farko da ake bukata daga dan siyasa shine ya zamo mara ban sha’awa.
- Kamus na Zantuka na Oxford
- Burtaniya Mai-girma ta rasa daular ta kuma har yanzu bata samu matsayi ba.
- Jawabi a West Point (5 ga watan Disamba, shekara ta 1962), in Vital Speeches, Janairu 1 ga wata, shekara ta 1963, page 163.
- Yakin Vietnam ta yi muni fiye da rashin ɗa’a - ta kasance kuskure ce.
- Rahoto a cikin Alistair Cooke, Wasika daga Amurka: shekara ta 1946 zuwa shekarar 2004 (2004), page 378.
- Ta yaya kasar Amurka zata yi nasarar samar da ‘yancin kai a duniya baki daya a yayin da ta gaza samar da ita ga muhimman marasa galihu a kasar ta.
- Civil rights in the USA, a shekara ta 1863 zuwa shekarar 1980,da shekarar 2001, Page 107.