Chloe Gong, (an haife ta a shekarar 1997 ko 1998), marubuciya ce, yar China, wacce bar New Zealand...
Zantuka
edit- … Ina ji kamar yin rayuwa sau biyu saboda ba wai kaman ina yawo da tarihin rayuwa na ta Twitter bane a lokacin da nike yawo a makaranta ko nike zuwa aji. Saboda haka Daliba Chloe da kuma Malama Chloe ba mutane biyu ne daban. Ina ga duk lokacin da nazo daf da wallafa littafi a lokacin ne wadannan fuskoki biyu ke hadewa da juna, musamman a lokacin da abokai na na aji suka samu labari game da littafi na. Tabbas wannan abu ne da nike fama da shi, wajen hana kaina daga gugar littattafai na kuma in zama ni duka, a’ah, “ai ba komai bane, kawai don sha’awa ne”, a yayin da zancen ya fito a tsakanin abokai na na makaranta da dai makamancin hakan, don kada in cire kaina daga dalibai sai in ce, “oh, ai yanzun nan naje aji” a yayin da nike tsakanin sauran marubuta.
- Akan zama marubuciya mai wallafa littattafai a yayin da take dalibar jami’a a cikin “Chloe Gong interview: Young blood in Young Adult” in The Writer (16 ga watan Oktoba, shekara ta 2020).