Chinua Achebe,(an haife Shi a ranar 16 ga watan Nuwamba, shekara ta 1930 zuwa Maris 21, shekara ta 2013), marubuci ne, dan Najeriy, mawaki, kuma mai sukar rubuce-rubuce. Littafinsa mai suna, Things Fall Apart (a shekarar 1958), shine littafi da aka fi karanta, a cikin littattafan zamani na Afurka.
Zantuka
edit- Duniya kamar rawar Juju ce. Idan kana so ka ganta da kyau, kada ka tsaya a waje daya.
- Arrow of God (a shekarar 1988).
Things Fall Apart (a shekarar 1958)
edit- Karin magana itace manja wanda ake amfani da ita cin magana.
- Babi na I.
- A yayin da wata ke haska wa gurgu ke marmarin tafiya.
- Babi na II (shafi na 14).
- Zamu rayu dukkanmu. Muna rokon rayuwa, ‘ya’ya, noma mai albarka da kuma farin ciki. Zaka samu abinda ke kyau a gare ka kuma nima zan samu abinda ke da kyau a gare ni. A bar shirwa ta huta kuma itama tsuntsuwar egret ta huta. Idan ɗaya ya ce wa daya ah ah, to fiffikensa ya karye.
- Babi na III (shafi na 22).
- Zuciya mai alfahari zata iya jurewa kowanne irin asara saboda wannan asara ba zata iya fasa alfaharin ta ba. Ya fi wahala da kuma ɗaci idan yayin da mutum ya faɗi shi kadai.