Ban Zhao (Chinese: 班昭; 49 – c. 120 CE) ta kasance masanin tarihi ’yar China kuma ‘yar siyasa. Itace mace ta farko masaniyar tarihi da aka sani.
Zantuka
edit- A shekaru goma sha hudu, ina da aure kuma na dauki abun kwashe shara da tsintsiyar dangin mijina. A koda yaushe ina tsoron cewa zan kawo ma dangi na abun kunya kuma in karawa dangin mijina wahalhalun su. Dare da rana ina jin ciwo a zuciya na amma na cigaba da aiki ba tare da nuna damuwa ta ba. A yanzu na san abubuwan da nike tsira daga tsoro irin wannan. Amma ina shakkan ko cewa ku ‘ya’ya na, baku da horo irin wanda ya kamata ya taimake ni. Saboda haka na rubuta wannan babi mai “Darasai ga Mata.” Ina fatan dukkanku zaku samu kwafi don kawunan ku.
- Sifar mace baya bukatar kyakyawan ko kuma cikakken fuska ko diri.
- Darussa ga Mata a cikin Pan Chao: A Girl of Old China by Paul Anderson (1953)