Ali Nuhu jarumin wasan kwaikwayo ne na Kannywood, mawakin, ɗan talla kuma ɗan kasuwa.An haife shi 15 ga watan maris 1974.

QuoteEdit
- An zo wajen
- daga wasan kwaikwayo
- Fim uku na fi so a rayuwa ta, amma kaman uba da 'ya'yansa bazan iya cewa ga wanda na fi so ba, akwai Sangaya, akwai Wasila akwai kuma Fil-azal
- Interview with Ali Nuhu, gaskiya da gaskiya Latest (Hausa Films & Music) 18 October, 2016. Retrieved 7th September 2022.
- Soyayya idan zaka so ɗan uwanka, so shi tsakaninka da mai sama Allah ko Rasulullah
- Waƙar Sangaya
- Shi jarumi (na wasan kwaikwayo) duk yaren da ya iya idan aka kirashi yayi fim a wannan yaren idan har ya cika jarumi, to zai je yayi. Idan ina jin Chanenci aka kirani inyi fim din China zanje inyi. Saboda saƙo ne zaka isar, yaren ne ya bambanta da kuma al'adun da ake yi a ciki.
- Interview with Ali Nuhu, gaskiya da gaskiya Latest (Hausa Films & Music) 18 October, 2016. Retrieved 7th September 2022.
- Duk fim ɗin da wani jarumi ya fito ko jaruma ta fito, to ba fa su bane. Rayuwarsu suke nunawa na wani, au mutumin kirki au kuma mutumin ba na kirki bane, idan na kirki ne za a ga abinda kirkin ya jawo masa, idan kuma ba na kirki bane za a ga abinda rashin kirkin ya jawo mai daga karshe. Wannan shine abinda ya kamata ya zama madubin dubawa a wajen mutane.
- Interview with Ali Nuhu, gaskiya da gaskiya Latest (Hausa Films & Music) 18 October, 2016. Retrieved 7th September 2022.
- Da farko dai, Nura ba jarumi bane mawaƙi ne, Ali Nuhu ba mawaƙi bane jarumi ne, kaga ba a ma shigo fage ɗaya da za a ce akwai wani abu makamancin gasa a tsakani ba balle har ace wani baya shiri da wani
- Tambaya akan dangartakansa da Nura M Inuwa: Interview with Ali Nuhu, gaskiya da gaskiya Latest (Hausa Films & Music) 18 October, 2016. Retrieved 7th September 2022.