Wq/ha/Alek Wek

< Wq‎ | ha
Wq > ha > Alek Wek

Alek Wek (an haife ta ranar 16 Afurelu 1977), ‘yar talla ce ‘yar asalin Kudan Sudan da Burtaniya, kuma dizaina wacce ta fara sana’ar talla tun tana shekaru 18 a 1995. Ana jinjina mata akan tasirin ta ga masana’antar talla ta fuskar kyawu. Ta fito da daga kabilar Dinka na Kudancin Sudan.

Alex Wek

Zantuka

edit
  • Babu shakka ba zan taba kasancewa a inda nike ba yau idan ba tare da taimkon ‘yan uwa, abokai, da wanda ban sani ba – da kuma UNHCR. Ina tuna wani jami’in UNHCR a Sudan, yana bata taimakon farko ga masu bukatar taimako a cikinmu. Har ya zuwa yau, ina ganin bulan tambarin yana sanya mun natsuwa, da kariya.
  • Ya kasance wani lokaci da na fara talla, da kuma aiki. Kuma abu daya da nike fadawa jami’ai na shine, idan zaku wakilce ni, ba zan zamo mai wayau ba kuma in kasance na wasu ‘yan shekaru ba. Sai ku dauke ni duka ko a bar shi.
  • “Na sani da duka zuciya ta cewa tana yin abun da ya dace ne ga mu. Amma hakan bai saukaka ciwon ba.”
  • Acikin shakara guda na tashi daga kididdigar ‘yar gudun hijira da ba kowa ba zuwa daya daga cikin fitattun fuskoki na duniya.