Wq/ha/Aishatu Madawaki

< Wq‎ | ha
Wq > ha > Aishatu Madawaki

Aishatu Madawaki', OFR (an haife ta a shekara ta alif 1951) ƴar jami'ar Najeriya ce kuma ƴar siyasa. Ita ce mace ta farko farfesa daga tsohuwar Jahohin Sokoto (wanda ya haɗa da a yau Jahar Sokoto, Jahar Zamfara da kuma Jihar Kebbi), yanki ne da musulunci ya mamaye a Arewacin Nijeriya. A shekarar 1999, gwamnatin Attahiru Bafarawa ya jagoranci naɗa ta kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban jama'a. Madawaki kuma mai fafutukar neman wakilcin matan Najeriya a fagen siyasa.

Zantuka edit

  • Domin wani ci gaba ya faru, dole ne a sami daidaiton jinsi.
    • [1] Daga taron ranar mata na duniya (Maris 8 2017)
  • Mata masu zaman lafiya ne, masu juriya, marasa lalacewa da kishin kasa.
    • [2] Daga taron ranar mata na duniya (Maris 8 2017)