Aishatu Madawaki, OFR (an haife ta a shekarar 1951).
malamar Najeriya ce kuma yar siyasa. Ita ce mace ta farko farfesa daga tsohuwar jahohin khalifancin Sakkwato a yankin da Musulunci ya mamaye a Arewacin Najeriya,Wand ya kunshi jihar Sokoto a yau da kebbi da kuma zamfara.A shekarar 1999 gwamnatin Attahiru Bafarawa ta nada ta kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma. Madawaki kuma mai fafutukar neman wakilcin matan Najeriya a fagen siyasa.
Zantuttuka
Domin duk wani ci gaba ya faru, to fa dole ne a sami daidaiton jinsi. [1] Daga na duniya
gangamin ranar mata (Maris 8 2017)
Mata masu zaman lafiya ne, masu juriya, marasa lalacewa da kishin kasa.
gangamin ranar mata (Maris 8 2017)