Aisha Buhari itace matar shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari.
Zantuttuka
- A cire tsoro ayi abinda ya dace
- Aisha Buhari ta fadi haka a lokacin da take yin martani game da harkokin tsaro da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a Arewacin Najeriya.
- Ina da ƙwarin gwiwar cewa sha'awarmu ta gaba ɗaya na inganta ilimin ƙananan yara da ƴan mata za ta iya faɗaɗa fiye da yadda take a yanzu.
- Aisha Buhari ta fadi haka a lokacin da take karɓar mambobin ƙungiyar masu dillancin magunguna ta ƙasar Amurka (NAPPSA).
- Yara suna da daraja kuma su ne makomarmu. Wajibi ne da alhakinmu a matsayinmu na iyali da al'umma mu ƙauna, kulawa da kuma kare su.