Wq/ha/Abdel Fattah el-Sisi

< Wq | ha
Wq > ha > Abdel Fattah el-Sisi

Abd El-Fattah Saeed Hussein Khalil El-Sisi, (an haife shi a ranar 19 ga watan Nuwamba,a shekara ta 1954), ɗan siyasan Masar ne, wanda shi ne shugaban Masar na shida kuma na yanzu, a ofis tun shekarar 2014.

Abdel Fattah el-Sisi

Zantuka

edit
  • Sojojin Masar babbar runduna ce ta kishin ƙasa, Sojojin Masar runduna ce mai daraja da taurin kai, kuma taurin kai yana fitowa daga girman kai. Jawabin el-Sisi a ranar bikin ƴantar da Sinai a ranar (28 ga watan Afrilun, shekarar 2013).
  • Ina so in gaya muku cewa, lokacin da sojojin Masar suka sauko kan tituna, suka zo don kare ku, suka zauna tsawon watanni 18, babu wani daga cikin sojojin da ya cutar da ku, dole ne a sare hannuwanmu idan za su cutar da ku. Ina maimaita wannan ne don ku sani, a cikin waɗannan watanni 18, akwai sojoji 150,000 a kan tituna. yana nufin tsawon kwanaki 500 tare da sojoji 150,000 a kan titi akwai yuwuwar miliyan 7.5, muna fama da rashin cutar da kowane Masari! Jawabin el-Sisi a ranar bikin ƴantar da Sinai wanda akai a ranar (28 ga watan Afrilun, shekarar 2013).
  •  
    Abdel Fattah el-Sisi
    Ba mu manta, kuma ba za mu manta ba. Jawabin da el-Sisi ya yi a ranar bikin ƴantar da Sinai wanda akai a ranar (28 ga watan Afrilun shekarar dubu biyu da goma sha uku 2013) game da sojojin Ƙasar da aka kashe a baya.