alA Raja cikakken sunan sa shine Andimuthu Raja, (an haife shi a ranar 26 ga watan Oktoba a shekara ta 1963) ɗan siyasa ne a ƙasar Indiya , daga yankin Tlamil Nadu, kuma memba ne na jam'iyyar Dravida Munnetra Kazhagam (DMK) ya fara shiga siyasa ta hanyar wakiltar yankin (perambalur) da kuma yankin (Nilgiris) a Majalisar tarayya ta Indiya.ya zama sananne ne a lokacin da aka naɗa shi ministan sadarwa da fasahar watsa labarai a cikin shekara ta dubu biyu da bakwai 2007. a ƙarƙashin gwamnatin UPA . Raja ya shiga cikin wata babbar badaƙalar cin hanci da rashawa da ke kira 2G Spectrum Scam inda akayi zargin cewa ya ba da lasisin sadarwa ba bisa ƙa'ida ba, wanda hakan yaa jawo wa gwamnati asarar manyan kuɗaɗe da suka kai biliyoyin daloli. Kotun ƙoli ta soke wadannan lasisin kuma ta bayyana cewa tsarin bada su be dace ba.An kama Raja a shekarar 2011 amma daga baya an wanke shi daga laifin saboda rashin hujja.
Zantuka
editSanatan Dharma ya kamata a kwatanta shi da cututtuka masu kyamar jama'a kamar HIV da kuturta