Curtis James Jackson III, (An haife shi a ranar 6 ga watan Yuli, a shekara ta 1975) a birnin New york Amurka, ya kasance fitaccen mawaƙin Rap ne, sannan kuma ɗan kasuwa,furodusa, kuma ɗan wasan kwaikwayo. Haka zalika Ya zama sananne a shekara ta 2003, bayan ya fitar da kundin waƙarsa me suna Get Rich or Die Tryin; wanda ya ƙunshi manyan waƙoƙi kamar In Da Club da 21 Questions. wannan kundin ya zama ɗaya daga cikin kundi mafi nasara a tarihi. An san 50 sent da salon waƙar rap mai ƙarfi da kuma labrinsa na rayuwa a titi,inda ya tsallake fadawa sharrin kisan kai har sau bakwai kafin ya fara sanin rayuwar duniya a matsayin mawaƙi. A shekara ta 2005, ya ƙara yin nasara da kundin waƙarsa na biyu.
Zantuka
edit- Ina so in bayyana gari na ga wanda bai taɓa zuwan sa ba fiye da waƙoƙin da suke siya da kuma hotunan da suke gani. Mutane suna son gaskiya, ko da kuwa ba zasu yarda da ita ba, suna son ta. Na bari kun sani cewa na sha harsashi guda tara ba wai don in saida waƙa ba, amma don kawai gaskiya ce. A duk lokacin da na zauna intabiyu mutane kan tambaye ni, to 50, ya ake ji idan aka sha harbin harsashi har tara?” Amma hakan ba ya riƙe ni ƙasa, azabar, ko kuma sa ran abunda na fuskanta. Kawai ba zai yiwu ba. Wannan shine tunani na kuma wadannan su ne abubuwan da ke faruwa. Wannan shi ne dalilin nike faɗan baitukan da nike faɗa. Wannan shi ne abunda ya faru a yayin da nike neman arziƙi kafin in mutu a Southside Queens.