ʿUmar ibn al-Khaṭṭāb ya kasance daya daga cikin sahabban Manzo Allah (SAW), kuma sarkin musulmi na biyu bayan halifancin Abubakar Assiddiq (RA).
Azanci
edit- Wanda ya yi kwaɗayi ya wulakanta kansa, wanda ya bayyanar da matsalarsa (asirinsa) ya yarda da kaskanci, wanda ya sallaɗa harshensa (ya saki harshensa) akan ransa ya wulaƙanta ta, rowa aibi ne, tsoro tawaya ne, talauci yana dakusar da kaifin hankali gabarin hujjarsa, mai karantawa baƙo ne a garin sa, gajiyawa aibi ne, dauriya jarunta ne, zuhudu jari ne, taka tsantsan garkuwa ne, madalla da aboki (ya zama) yarda, ilmi gado ne mai daraja, ladabi ado ne mai sabuntuwa, tunani karau ne mai tsafta, kirjin mai hankali akwatin sirrinsa, sakin fuska tarkon soyayya ne, kawo hanzari kabarin aibobi ne.
- Ka zama cikin fitina kamar ɗan saniya mai shan nono ba shi da baya balle a hau kuma ba shi da hantsa balle a tatsa.
- Amincewa juna maɓoyar aibi ne, duk wanda ya amincewa kansa fushi zai ƙaru a kansa, sadaka magani ce mai warkarwa, ayyukan bayi na ibada a magaggauciya [Duniya] natsuwar (farin cikin) ido ne a majinkirciya (Lahira).
- Abin mamaki ga mutum, yana gani ta hanyar kitse, yana Magana ta hanyar tsoka, yana ji ta hanyar kashi, kuma yana numfashi ta hanyar kafa.
- dan ka sami iko akan makiyin ka, to ka sanya afuwa gare shi ta zama godiya ga Allah akan wannan iko da ka samu a kansa.
- Idan farkon ni'imomi suka zo muku, to kada ku zamo masu nisanta da karancin godiya.
- Wanda na kusa ya tozarta shi, sai a yalwata masa samun na nesa.
- Ba duk wanda aka fitanar ba ne abin zargi.
- Abubuwa suna rusunawa gaddarawa, har sai ajali ya yi halinsa.
- Ya fada game da wadanda suka ki fita yaki tare da shi: sun bar gaskiya, ba su taimaki barna ba.
- Wanda ya yi tafiya a tsakatsakin burinsa, ya hadu da ajalinsa.
- Ku zode wa ma'abota mutunci kananan laifuffukansu, domin ba wanda zai yi kuskure daga cikinsu sai hannunsa ya kasance a hannun Allah yana daukaka shi.
- An gwama tsorata da rasawa (idan ka ji tsoron yin abu ka rasa shi), kunya kuma da hani (haka nan wanda ya faye jin kunyar abu sai ya rasa), dama tana wucewa ne kamar wucewar gajimare, ku riki damar alheri
- Muna da hakki idan an ba mu shi, in ba haka ba (ba a ba mu ba) sai mu hau kan duwainiyar rakumi, (wato sai mu dau hakuri) komai daren dadewa. Hawa duwainiyar rakumi gun larabawa alama ce ta kaskantar da mai hakki, wato wanda aka goya a baya rakumi yana zama dai dai kan duwainiyarsa ne ba gaba ba, wato kamar yaro ko bawa da ake goyawa a bayan rakumi ne
- Wanda aikinsa ya jinkirtar da shi, dangantakarsa ba zata daukaka shi ba.
- Yana daga kaffarar zunubai taimakon wanda yake cikin kunci, da yaye wa mai bakin ciki bakin cikinsa.
- Ya kai dan adam, idan ka ga ubangijinka yana bibiyar ni'imarsa a gareka kana saba masa, to ka kiyaye shi.
- Ba wanda ya taba boye wani abu sai ya bayyana a harshensa da fadin fuskarsa.
- Tafi tare da ciwonka matukar zai tafiyu tare da kai. (Amma idan ba zaka iya ci gaba da aiki ba sai ka huta)
- Mafificin zuhudu, shi ne boye zuhudu.
- Idan ka kasance cikin tahowa da-baya-da-baya, mutuwa kuma cikin gabatowa gaba, to lallai ya mamakin saurin haduwa!
- Hattara hattara! Na rantse da Allah ubangiji ya boye (kurakurai) kai ka ce ya riga ya gafarta.
- An tambaye shi game da imani sai ya ce yana kai ginshiakai hudu ne: akan juriya, da yakini, da adalci, da jihadi: Hakuri yana kan rassa hudu: akan shauki, da tsoro, da zuhudu, da taka-tsantsan: wanda ya so aljanna zai fidiye daga shahawaice-shahawaice, wanda ya ji tsoron wuta zai nisanci haram, wanda ya yi gudun duniya zai ga saukin musibu, wanda ya yi sauraron mutuwa zai gaggauta zuwa aikata alherai.
- Yakini yana kan rassa hudu ne: akan kaifin kwakwalwa, da fassarar hikima, da wa'aztuwa da daukan darasi, da bin dabi'un magabata: wanda ya ke da kwakwalwa hikima zata bayyana gareshi, wanda hikima ta bayyana gareshi zai dau darasi, wanda ya dau darasi, kamar yana cikin na farko ne.
- Adalci yana kan rassa hudu ne: akan zurfin fahimta, da sirrin ilimi, da kayen ni'ima, da kafaffen hakuri: duk wanda ya fahimata zai san zurfafan ilimi, wanda ya san zurfafan ilimi zai zo da komai daga hukunce-hukunce, wanda ya yi hakuri ba zai yi shisshigi da wuce gona da iri a al'amuransa ba, kuma zai rayu cikin mutane abin yabo.
- Jihadi kuma Yana Kan rassa hudu ne: Akan umarni da kyakkyawa, da hani daga mummuna, da gaskiya a ko'ina, da kin fasikai. Wanda ya yi umarni da kyakkyawa ya karfafi muminai, Wanda ya hana mummuna ya turmuza hancin munafukai a kasa (ya bakanta ran munafikai), Wanda ya yi gaskiya a ko'ina ya sauke nauyin da yake Kansa, Wanda ya ki fasikai ya yi fushi saboda Allah Allah zai yi fushi saboda shi ya kuma yardar da shi ranar sakamako.
- Kafirci yana kan shika-shikai hudu ne: akan zurfafawa, da jayayya, da karkata, da sabawa: wanda ya zurfafa ba zai karkata zuwa ga gaskiya ba, wanda jayayyarsa ta yi yawa da jahilci makantarsa ga barin gaskiya zata dawwama, wanda ya karakace mummuna zai zama kyakkyawa gunsa kuma kyakkyawa ya zama mummuna gunsa ya yi maye mayen bata, wanda ya saba hanyoyinsa zasu kulle masa (su yi tsauri), al'amarinsa ya tsananta, mafitarsa ta yi wahala ta kuntata.
- Kokwanto yana kan rassa hudu ne: akan jayayya, da tsoro, da kai-kawo, da mika wuya: wanda ya sanya jayayya ta zama masa al'ada darensa ba zai waye ba, wanda abinda yake gabansa ya tsorata shi zai sallama (tankwasa ya rusuna akan kafafunsa) a gabansa, wanda ya kai-kawo a kokwanto kofatun shedanu sa tattaka shi, wanda ya mika wuya ga halakar duniya da lahira zai halaka a cikinsu.
- Mai aikata alheri ya fi alheri alheri, mai aikata sharri ya fi sharri sharri. (wato mai aikata alherin shi ne mafi girman alheri daga alheri shi kansa, haka ma mai sharrin shi ya fi sharri zama sharri)
- Ka zama mai sauki kada ka zama mai almubazzaranci, ka zama mai tsakaitawa, kada ka zama mai kwauro.
- Mafi girman wadata barin buri.
- Wanda ya gaggautawa mutane (wato farkon saninsu da shi) da abinda suke ki, sai su fadi abinda ba su sani ba game da shi.
- Wanda ya tsawaita buri zai munana aiki.
- Yana mai gaya wa dansa Hasan (A.S): ya kai dana ka kiyaye hudu daga gareni, matukar ka yi aiki da su ba abinda zai cutar da kai: Hakika mafi wadatar wadata shi ne hankali, mafi girman talauci shi ne wauta, mafi dimuwar dimuwa shi ne ji-ji-da-kai, mafi girman nasaba shi ne kyawun dabi�u.
- Ya dana na hana ka abota da wawa, domin shi ya kan so ya amfane ka sai ya cutar da kai. Kuma na hana ka abota da marowaci, domin shi ya barka shi ne ya fi da bukatuwar da zaka zama kana yi masa.
- Na hanaka abota da fajiri, domin shi zai iya sayar da kai da dan kankanin abu. Na hana ka abota da makaryaci, domin shi kamar sururi ne: da yake kusantar da nesa gareka, yake nesantar da kusa gabarinka.
- Babu wani kusanci da Allah da nafiloli, idan ta cutar da farillai.
- Harshen mai hankali yana bayan zuciyarsa, zuciyar wawa tana bayan harshensa
- Farin ciki ya tabbata ga Wanda ya tuna lahira, ya yi aiki saboda hisabi, ya wadatu da kadan, ya yarda da hukuncin ubangijinsa.
- Mummuna da zai bata maka rai shi ya fi kyakkyawa da take kayatar da kai a wajan Allah.
- Kimar mutum tana daidai gwargwadon himmarsa, gaskiyarsa kuma tana daidai mutuncinsa, jarumtakarsa tana daidai gwargwadon karfinsa, kamewarsa tana daidai gwargwadon kishinsa.
- Rabauta da daukar niyya ne, niyya kuma tana daga tuntuntunin ra'ayi, ra'ayi kuma yana samuwa da kewaye sirrai.
- Ku ji tsoron hayewar mai karimci idan ya ji yunwa, marowaci kuma idan ya koshi.
- Zukatan maza dabbar daji ce, wanda ya saba da ita sai ta kusanto gareshi.
- Ka rabauta kwarai matukar aibinka ya zama asirtacce.
- Wanda ya fi cancanta a cikin mutane ya yi afuwa shi ne wanda ya fi ikon ukuba daga cikinsu.
- Kyauta ita ce wacce take tun farko, amma idan ta kasance domin an roka ne to wannan kunya ce da gudun zargi.
- Babu wadata kamar hankali, babu talauci kamar jahilci, babu gado kamar ladabi, babu mai taimako kamar shawara.
- Hakuri kala biyu ne: hakuri akan abin da kake ki, da hakuri gabarin abinda kake so.
- Wadata acikin bakunta zaman gari ne, talauci a cikin zaman gari bakunta ce.
- Wadata dukiya ce da ba ta karewa.
- Dukiya mabubbugar shahawa ce.
- Wanda ya yi maka gargadi kamar wanda ya yi maka albishir ne.
- Harshe zaki ne, idan aka bar shi sai ya yi cizo.
- Mace kunama ce harbinta mai zaki ne.
- Idan aka gaishe da kai da gaisuwa to ka amsa da mafi kyawunta, idan aka mika maka hannu ka saka mata da abin da ya zarta nata, amma duk da haka fifiko yana ga wanda ya fara.
- Mai ceto shi ne ginshikin (karfin) mai nema.
- Mutanen duniya kamar matafiya ne da ake tafiya da su alhalin suna bacci.
- Rashin masoya bakunta ne.
- Kubucewar bukata ya fi sauki daga nemanta wajan wadanda ba ma'abotanta ba.
- Kada ka ji kunyar bayar da kadan domin hanawa ya fi shi karanci.
- Kamewa (gabarin tambaya) adon talauci ne, godiya adon wadata ce.
- Idan babu abinda kake nema (ko kuma abin da kake so bai wakana ba) to kada ka damu da yaya ka kasance.
- Ba yadda zaka ga jahili sai dai imma mai wuce gona da iri ko mai gazawa.
- Idan hankali ya cika Magana sai ta yi karanci.
- Zamani yana tsofar da jiki, yana kuma jaddada buri, yana kusantar da mutuwa, yana nesantar da burace-burace, wanda ya same shi ya jigata, wanda ya kubuce masa ya wahala.
- Wanda ya sanya Kansa shugaba ga mutane to yana kansa ya fara koyar da kansa kafin ya koyar da waninsa, ya zama tarbiyyatar da zuciya kafin ya tarbiyyatar da harshensa, mai koyar da kansa mai ladabtar da ita shi ya fi cancanta da girmamawa fiye da mai koyar da mutane mai ladabtar da su.
- Lumfashin mutum takunsa ne zuwa ajalins.
- Duk abin kididdiga mai tawaya ne, kuma duk abin da ake sauraro mai zuwa ne.
- Idan al'amura suka rikitar suke cakude sai a kiyasta karshenta da farkonta.
- Imam Ali (A.S) ya fadi kwatankwacin hakan: Hikima bataccen kayan mumini ne, ka riki (karbi) hikima koda kuwa daga munafukai ne.
- Imam Ali (A.S) ya ce: Kimar kowane mutum shi ne abin da yake kayatar da shi.
- Imam Ali (A.S) ya ce: na yi muku wasici da abubuwa biyar da zaku yi tafiye-tafiye da rakuma domin ku same su da sun cancanci hakan: kada wani daga cikinku ya kaunaci kowa sai ubangijinsa, kuma kada ya ji tsoro sai zunubansa, kada wani ya ji kunya idan aka tambaye shi abin da bai sani ba ya ce: ban sani ba, kuma kada wani ya ji kunya idan bai san wani abu ba ya nemi saninsa.
Kuma game da hakuri, hakika misalin hakuri ga imani kamar misalin kai ne ga jiki, kuma babu wani alheri ga jikin dab a shi da kai, ko kuma imanin dab a shi da hakuri tare da shi.
- Imam Ali (A.S) ya ce da wani mutum da ya yawaita yabonsa, kuma alhalin Imam (A.S) ya kasance yana sanin cewa (shi wannan mutumin karya yake yi a zuciyarsa): Ni ina kasan abin da ka fada, kuma sama da abin da yake cikin ranka nake.
- Imam Ali (A.S) ya ce: ragowar takobi (mutanen da suka rage bayan yaki domin 'yancinsu) su ne wadanda jama'arsu ta fi wanzuwa, kuma suka fi yawaitar yaduwar 'ya'ya.
- Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya bar fadin: ban sani ba, to an samu makasarsa.
- Imam Ali (A.S) ya ce: ra'ayin dattijo ya fi soyuwa gareni fiye da karfin jarumtakar saurayi. An ruwaito a wata ruwaya fiye da halartar saurayi (a wajen yaki).
- Imam Ali (A.S) ya ce: Ina mamakin wanda yake yanke kauna alhalin akwai istigfari tare da shi.
- Abu Ja'afar Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ruwaito daga Imam Ali (A.S) ya ce: Akwai aminci biyu masu tseratarwa daga azabar Allah (S.W.T) da suka kasance a fadin kasa, gashi hakika an riga an dauke dayan, don haka ku yi riko da dayan: amma wanda aka dauke shi ne manzon Allah (S.A.W).
Amma wanda ya wanzu shi ne istigfari, ubangiji madaukaki ya ce: Allah bai kasance mai yi musu azaba ba alhalin kai kana cikinsu, kuma Allah bai kasance mai yi musu azaba ba alhalin suna istigfari.
- Imam Ali (A.S) ya ce: malamin da lallai shi ne ya isa malami shi ne wanda bai sanya mutane sun yanke kauna daga rahamar Allah ba, kuma bai sanya su yanke kauna daga tausayawar Allah ba, kuma bai amintar da su daga makircin (azabar) Allah ba.
- Imam Ali (A.S) ya ce: mafi kaskancin ilimi shi ne wanda ya tsaya a kan harshe kawai, mafi daukakarsa shi ne wanda ya bayyana a kan gabobi da sassan asali na jiki.
- Imam Ali (A.S) ya ce: Hakika wadannan zukata suna kosawa kamar yadda jikunkuna suke kosawa, don haka ku nema mata hikima mai dadi.
- Imam Ali (A.S): kada xayanuk Ya ce: ya ubangiji ni ina neman tsarinka daga fitina, domin babu wani mutum sai yana tare da wata fitina, sai dai dukkan wanda zai nemi tsari to ya nemi tsari daga masu vatarwa na daga fitinu, haqiqa Allah maxaukaki yana cewa: Ku sani cewa haqiqa dukiyoyinku 'ya'yanku fitina ne, ma'anar wannan shi ne; cewa shi maxaukaki yana jarraba su da dukiyoyi da 'ya'ya domin ya bayyanar da mai fushi da arzikinsa da kuma wanda ya yarda da rabonsa, duk da kuwa ubangiji maxaukaki ya fi su sanin kawukansu, sai dai domin ya bayyanar da ayyukan da, da sun e zasu cancanci lada da uquba, domin wasu suna son maza kuma suna qin mata, wasu kuma suna son juya (havaka) dukiya ne suna qin tawayar halal.
Wannan yana daga cikin maganganu masu qayatarwa da aka ji daga gareshi (A.S) a tafsiri.
- An tambayi Imam Ali (A.S) game da alheri mene ne shi? Sai Imam Ali (A.S) ya ce: alheri ba shi ne dukiyarka da 'ya'yanka su yawaita ba, sai dai alheri shi ne; iliminka ya yawaita, kuma haqurinka ya girmama, kuma ka yi alfahari ga mutane da bautar ubangijinka, idan ka kyauta sai ka godewa Allah, idan kuma ka yi munana sai ka nemi gafarar Allah. Kuma babu wani alheri a duniya sai ga mutane biyu: mutumin da ya yi zunubi yana mai riskarsa da yin tuba, da kuma mutumin da yake gaggawa cikin aikata alheri. kuma aiki ba ya qaranta tare da taqawa, yaya kuwa abin da ake karva zai qaranta?
- Imam Ali (A.S) ya ce: haqiqa mafi cancantar mutane ga annabawa su ne mafi sanin abin da suka zo da shi, sannan sai ya karanta ayar nan haqiqa mafi cancantar mutane da ibrahim su ne waxannan da suka bi shi, da wannan annabi da kuma waxannan da suka yi imani, kuma Allah shi ne majivancin muminai.
Sannan sai Imam Ali (A.S) ya ce: haqiqa masoyin Muhammad (S.A.W) shi ne; wanda ya bi Allah koda kuwa nasabarsa ta nisanta, kuma maqiyin Muhammad (S.A.W) shi ne wanda ya savawa Allah (S.W.T) koda kuwa nasabarsa ta kusanta!
- Imam Ali (A.S) ya ce: -alokacin ya ji wani mutum daga Haruriyya[4] yana sallar dare, yana karatun kur'ani, sai ya ce: Bacci a kan (bisa) yaqini ya fi salla cikin kokwanto.
- Imam Ali (A.S) ya ce: ku sanya wa labari hankali idan kuka ji shi hankalin kiyayewa ba hankalin ruwaitowa ba, ku sani haqiqa masu ruwaito ilimi suna dayawa, amma kuma masu kiyayewa (sanya masa hankali) 'yan kadan ne.
- Imam Ali (A.S): a lokacin ya ji wani mutum yana cewa; "Inna lil-Lahi wa'inna ilaihi rajiuun" sai ya ce: Haqiqa fadinmu cewa: "Inna lil-Lahi� furuci ne a kan kawukanmu ga mulkin Allah, kuma faxinmu; Wa inna ilaihi raji'un furunci ne a kan kawukanmu da halaka.
- Imam Ali (A.S) ya ce: A lokacin da wasu mutane suka yabe shi a gabansa-: Ya ubangiji kai ne mafi sani da ni daga kaina, kuma ni ne mafi sani da kaina fiye da su, ubangiji ka sanya ni fiye da yadda suke tsammani, ka gafarta mana abin da ba su sani ba.
- Imam Ali (A.S) ya ce: Ba yadda biyan buqatu zai daidaitu sai da abubuwa uku: da qaranta ta domin ta girmama, da kuma neman voye ta domin ta bayyana, da kuma gaggauta ta domin ta yi sannu-sannu.
- Imam Ali (A.S) ya ce: Da sannu wani zamani zai zo wa mutane da ba a kusantarwa a cikinsa sai annamimi, kuma ba a qayatarwa sai fajiri, kuma ba a raunatarwa sai mai adalci, suna ganin sadaka a matsayin abin biyan bashi, kuma sadar da zumunci a matsayin gori, kuma ibada domin neman fifiko a kan mutane! A lokacin ne sarauta (tafiyar da mulki) zata kasance da shawarar bayi, da jagorancin yara, da kuma tsarawar fixiyayyun mutane!
- Imam Ali (A.S) ya ce: Yana sanye da wani zani tsoho da ya qoqe, sai aka yi masa magana game da haka. Sai (A.S) ya ce: Zuciya tana tsoratuwa saboda shi, kuma rai tana qasqantuwa da shi, kuma muminai suna koyi da shi.
- Daga Nuf al'bikaliyyu, ya ce: Na ga Imam Ali (A.S) a wani dare, ya fito waje daga kan daga shimfixarsa, sai ya saurara kaxan sannan sai ya ce: Ya kai Nuf, shin kana bacci ne ko kuma kana farke?
Sai na ce: Ina farke ne ya amirul muminin.
Sai ya ce: Ya kai Nufu, Farin ciki ya tabbata ga masu gudun duniya, masu kwaxayi a lahira, waxannan su ne mutanen da suka riqi qasa mashimfixa, turvayarta kuma shimfixa, ruwanta kuma daddaxa, Kur'ani kuwa alami[6], addu�a kuwa tufafi, sannan sai suka yayyaga (kekketa) duniya irin yayyagawar nan (irin ta tafarkin) da Masihu (A.S) (annabi Isa) ya yi mata.
Ya kai Nufu, Haqiqa Dawud (A.S) ya tsaya daidai irin wannan awar ta dare, sai ya ce: wannan sa'a ce da babu wani bawa da zai kira Allah ya yi addu'a a cikinta sai an amsa masa, sai dai idan ya kasance mai karvar haraji ne, ko kuma xan leqen asiri, ko kuma xan sanda, ko mai buga ganga, ko kuma makaxi.
- Imam Ali (A.S) ya ce: Haqiqa Allah maxaukaki ya farlanta muku wasu farillai to kada ku tozarta ta, kuma ya shata muku iyaka kada ku shige ta, kuma ya hana ku wasu abubuwan to kada ku keta (kutsa) su, sannan ya yi shiru gabarin wasu abubuwa da bai bar su ba don mantuwa, to kada ku xora wa kanku nauyinsu.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Mutane ba su taba barin wani abu na lamarin addininsu ba saboda gyara duniyarsu, sai Allah ya bude musu abin da ya fi shi cutarwa.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Da yawa malamin da jahilcinsa ya kashe shi, kuma iliminsa yana tare da shi ba ya amfanarsa.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Hakika an damfara wata tsoka da jijiyar mutum da take ita ce mafi ban mamakin cikinsa: wannan ita ce; zuciya, ga ta da tarin hikimomi, da kuma abubuwan da suka sassaba mata, idan ya samu kansa cikin yin kauna sai kwadayi ya kaskantar da shi, idan kuwa ya samu rarumar kwadayi sai zari ya halaka shi, idan kuma yanke kauna ya mamaye shi sai bakin ciki ya kashe shi, ida kuwa ya samu fushi sai takaici ya tsananta masa, idan kuwa yarda ta rabautar da shi sai ya manta da kiyayewa, idan kuwa tsoro ya kama shi sai hattara ta shagaltar da shi, idan ya samu yalwar aminci sai gafala ta yi masa kwace, idan musiba ta auka masa sai raki ya kunyata shi, idan ya samu dukiya sai ya yi takama, idan talauci ya cije shi sai bala'i ya shagaltar da shi, idan yunwa ta raunata shi sai raunin jiki ya gurfanar da shi, idan kuwa koshi ya yi masa yawa sai katon ciki ya kuntata masa (lumfashi), don haka ne duk wani takaitawa gareshi mai cutarwa ce, duk wani wuce gona da iri nasa mai batawa ne.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Mu ne matasan tsakiya, da su ne wanda yake zuwa yake riska, garesu ne mai shisshigi yake komawa.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Ba mai tsayar da lamarin Allah sai wanda ba ya kagowa, ba ya kamantuwa, ba ya bin kwadayi.
- Imam Ali (a.s) -Lokacin nan Sahalu dan Hunaif Ansari ya rasu a Kufa bayan ya dawo daga Siffain, ya kasance daga mafi soyuwar mutane a gunsa, sai ya ce: Da dutse ya so ne, da ya tsattsage.
{Wato; masu sona bala'i yana yi musu yawa, yana gaggauta musu, wannan ya yi kama da fadinsa mai zuwa}
- Imam Ali (a.s) ya ce: Wanda ya so mu Ahlul Baiti (a.s) to ya tanadi bargon talauci.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Babu Dukiyar da ta fi hankali amfani, kuma babu wata kadaita da ta fi jin kai dimuwa, babu hankalin da ya kai shirya lamurra, babu wata kyauta da ta kai takawa, babu wani aboki da ya kai kyawun halaye, babu gadon da ya kai ladabi, babu jagoran da ya kai dacewa, babu kasuwancin da ya kai aiki na gari, babu ribar da ta kai lada, babu tsantsenini da ya kai tsayawa gun shubuha, babu wani zuhudun da ya kai gudun haram, kuma babu ilimin da ya kai tunani, babu ibadar da ta kai yin farilla, babu imanin da ya kai kunya da hakuri, babu nasaba da ta kai kaskantar da kai, babu daukakar da ta kai ilimi, babu taimakon da ya kai yin shawara.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Idan gyara ya mamaye zamani da mutanensa, sannan sai wani mutum ya munana zato ga wani mutum da babu wani kuskure da ya bayyana gareshi, to ya zalune shi! Amma idan barna ta mamaye zamani da mutanensa, sai wani mutum ya kyautata wa wani mutum zato, to ya yaudari kansa.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Yaya muka same ka ya Sarkin Muminai? Sai ya ce: Yaya wanda yake karewa da wanzuwarsa zai kasance, kuma yake cutuwa da lafiyarsa, kuma ake zo masa ta inda yake aminta!.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Da yawa wanda aka yi wa istidraji da kyautata masa, kuma da mai ruduwa da suturta masa, da mai fitinuwa da kyakkyawan yabon sa! Babu wani mutum da aka jarraba da wani abu kamar yi masa jinkiri.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Mutum biyu sun halaka a kaina: Mai so mai wuce gona da iri, da mai ki mai gaba.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Tozarta dama, bakin ciki ne.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Misalin duniya kamar macijiya ce: Taba ta yana da taushi, amma guba mai halakarwa ce a cikinta, mai ruduwa jahili yana son ta, mai kula da hankali yana gudun ta.
- Imam Ali (a.s) ya fada Yayin da aka tamaye shi game da Kuraishawa-: Amma Banu Makhzum su kanshin Kuraishawa ne, muna son zancen mazajensu, kuma muna aurar matansu. Amma Banu Abdusshams, Su ne mafi nisan ra'ayi, kuma mafi hanin abin da yake garesu. Amma mu, mu ne mafi sakin hannu, mafi kyautar rayukanmu yayin mutuwa, su ne mafi yawa, mafi makirci, mafi munani, mu kuma mu ne mafi fasaha, mafi rangwame, mafi kyawu.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Akwai bambanci tsakanin ayyuka biyu: Aikin da dadinsa yake tafiya, wahalarsa ta rage, da aikin da wahalarsa take tafiya, ladansa ya rage.
- Wani mutum ya bi wata janaza yana mai yin dariya, sai Imam Ali (a.s) ya ce: Kamar dai mutuwa a cikin (duniya) an rubuta ta ne a kan waninmu, kamar dai gaskiya a cikinta ta wajabta kan waninmu ne, kamar dai wannan abin da muke gain na matattu tafiya ce da bayan jimawa zasu dawo gunmu! Muna binne jikinsu, muna cin gadonsu, kamar dai mu zamu dawwama ne, mun mance dukkan wani mai azi, an jefe mu da dukkan lalacewa!!.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Farin ciki ya tabbata ga wanda ya kaskan da kansa, ya dadada nemansa, ya kyautata halinsa, ya ciyar da abin da ya rage na dukiyarsa, ya kuma kame harshensa, ya nesantar da sharrinsa daga mutane, kuma sunna ta ishe shi, ba a danganta shi da bidi'a ba.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Kishin mace kafirci ne, Kishin namiji kuwa imani ne.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Zan yi bayanin musulunci da bayanin da wani bai yi ba kafina: Musulunci shi ne mika wuya, mika wuya kuwa shi ne yakini, yakin kuwa shi ne gaskatawa, gaskatawa kuwa shi ne furuci, furuci kuwa shi ne bayarwa, bayarwa kuwa shi ne yin aiki.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Ina mamakin marowaci yana gaggauto da talaucin da yake guje masa, kuma wadatar da yake nema tana kubuce masa, sai ya yi rayuwar talakawa a duniya, kuma a yi masa hisabin masu wadata a lahira. Kuma ina mamaki ga mai girman kai wanda ya kasance mani a jiya, gobe kuma mushe ne. Kuma ina mamakin wanda yake kokwanton samuwar Allah, alhalin yana ganin halittar Allah. Kuma ina mamakin wanda ya manta da mutuwa alhalin yana ganin mutuwa. Kuma ina mamakin wanda ya yi musun tashin karshe, alhalin yana ganin tashin farko. Kuma ina mamakin mai raya gidan karewa, yana barin gidan wanzuwa.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Wanda ya takaita a aiki sai a jarrabe shi da bakin ciki, kuma babu wata bukata ga Allah ga wanda Allah ba shi da wani rabo a cikin ransa da dukiyarsa.
- Imam Ali (a.s) ya ce: Ku kiyayi sanyi a farkonsa, ku kuma fuskance shi a karshesa, ku sani yana yi wa jiki abin da yake yi wa shuka, farkonsa yana kuna, karshensa yana yin ganye. (Yana taba jiki a karshensa bayan ya saba da shi, sai ya kasance ya fi sauki ga jiki a lokacin).
- Imam Ali (a.s) ya ce: Girman mahalicci gunka, yana kaskantar da abin halitta a idanuwanka.
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Allah yana da wani mala'ika da yake kira kowace rana cewa; Ku Haifa domin mutuwa, ku tara domin karewa, ku gina domin rushewa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Duniya gidan wucewa ne zuwa gidan tabbatuwa, mutane a cikin iri biyu ne: Mutumin da ya sayar da ransa sai ya halaka ta, da mutumi da ya sayi ransa sai ya 'yanta ta".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Aboki ba ya zama aboki sai ya kiyaye abokinsa cikin abubuwa uku: Cikin bala'insa, da boyuwarsa, da mutuwarsa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Salla kusancin dukkan mai tsoron Allah ce, kuma hajji jihadin duk wani mai rauni ne, kuma kowane mutane yana da zakka, amma yin azumi ne zakkar jiki, kyakkyawan zaman aure kuma shi ne jihadin mace".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku nemi saukar arziki da yin sadaka, kuma duk wanda ya yi yakini da mayewa to zai kyautata bayarwa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Taimako yana sauka gwargwadon bukata ne".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk mutumin da ya tsakaita a -rayuwa- ba zai yi talauci ba".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Karancin Iyali dayan Yalwa ne guda biyu, Soyayyar (mutane) rabin hankali ne, Bakin ciki rabin tsufa ne".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakuri yana sauka ne gwargwadon musiba, wanda kuwa ya buga hannunsa a kan cinyarsa gun wata musiba, hakika ya shafe ladansa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Sau da yawa mai azumin da ba shi da komai a azuminsa sai kishirwa, kuma da yawa mai tsayuwar sallar dare ba shi da komai sai wahala, madalla da baccin masu hankali da cin abincinsu!".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku kiyaye imaninku da sadaka, ku kare dukiyoyinku da zakka, ku kare tunkudowar bala'i da addu'a".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutum boyayye ne karkashin harshensa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Mutumin da bai san kimarsa ba, ya halaka".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Kowane mutum yana da karshe mai zaki ko mai daci".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wani abu mai zuwa yana da komawa, kuma abin da ya koma ya juya baya kai ka ce bai kasance ba".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai hakuri ba ya rasa rabauta ko da kuwa zamani ya tsawaita gareshi".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Mai yarda da aikin wasu mutane kamar mai shiga cikinsu ne tare da su, ku6ma duk wani mai shiga cikinsu yana da zunubi biyu: Zunubin aiki da shi, da zunubin yarda da shi".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku kiyaye alkawura gun ma'abotanta".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku yi biyayya ga wanda ba a yi muku uzurin jahilcinsa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika an nuna muku idan kun nemi gani, kuma an shiryar da ku idan kun nemi shiryuwa, kuma an jiyar da ku idan kun nemi ji".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Dora wa dan'uwanka nauyi da kyautata masa, ka kore sharrinsa da yi masa ni'ima".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya jefa kansa wurin tuhuma, kada ya zargi wanda ya munana masa zato".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi mallaka zai yi danniya, wanda ya kayatar da ra'ayinsa zai halaka, wanda ya yi shawara da mazaje zai yi tarayya da su a hankulansu, wanda kuma ya boye sirrinsa to zabin yana hannunsa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Talauci shi ne mafi girman mutuwa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya biya hakkin wanda ba ya biyan hakkinsa to hakika ya bautar da shi".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu biyayya ga abin halitta cikin sabon mahalicci".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Ba a aibata mutum da jinkirta hakkinsa, sai dai ana aibata wanda ya karbi abin da ba nasa ba.
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Jin kai yana hana neman daduwa".
- Imam Ali (a.s) ya ce: "Lamarin kusa yake, ga abota kadan ce".
Manazarta
edit- "Babin Zababbu Daga Hikimomin Amirul Muminina (A.S) Da Wa�azozinsa, Ya Hada Da Amsoshin Tambayoyinsa Da Gajerun Kalamansa Da Makamantansu". balaghah.net. Retrieved 20 August 2022.