Sir `Abdu'l-Bahá `Abbás Effendí (23 Mayu 1844 – 28 Nuwamba 1921), wanda aka fi sani da Abdu'l-Bahá (abdol-ba-haa), ya kasance ɗa ga wanda ya samo Addinin Baha’i.
Zantuka
edit- So itace sirrin wahayin Allahntaka!
So itace hasken bayyanuwa!
So cikan burin ruhi ne
So numfashi ne na ruhi mai tsarki wanda aka sanya a cikin ruhin dan-Adam!
So itace silar bayyanuwar gaskiya (Ubangiji) a cikin wannand duniya mai ban mamaki.!
So itace cigaban gaskiyar yiwuwar abubuwa ta hanyar halittun Allah!
So hanya ce ta dumbin farin ciki a duka duniyar ababen more rayuwa da kuma duniyar ruhi!
So haske ne sosai mai jagoranci a cikin duhu!
So wata alaka ce tsakanin mahalicci da kuma halitta a can duniyar ciki!
So itace sanadiyyar cigaba ga duk wani mutum mai haskawa
So itace silar doka a wannan duniyar mai fadi ta Allahu!
So itace doka guda daya wacce take janyo kuma ta gudanar da tsari a tsakanin dukkanin halittu!
So wata karfin iko ce ta duniya a tsakanin duniyoyi da taurari da ke haskakawa a samaniya!
So itace silar budewar zuciya mai bincike, na sirruka da mabuwayi ya adana a wannan duniya!
So itace ruhi rayuwa a cikin jiki ma’abocin falala a wannan duniyar!
So itace silar wayewar kasashe a cikin wannan rayayyar duniyar!
So itace daukaka mafi karamci a kowacce kasa na gari!