Wq/ha/Bella Rwigamba

< Wq‎ | ha
Wq > ha > Bella Rwigamba

Bella Rwigamba 'yar kasar Ruwanda ce wacce Babbar Masaniyar Dijital ce a Ma'aikatar Ilimi ta kasar. Tana da digiri na biyu a fannin Tsarin Cigaban Bayanai daga Jami'ar HAN dake kasar Netherlands da kuma BBA a Fannin Tattalin Bayanai daga Jam'iar Adventist na Tsakiyar Afurka.

Zantuka edit

  • Iyaye zasu iya ganin abunda ake koyarwa a aji sannan zasu iya taimakawa yara a wajen bita da aikin gida. Dalibai kawai suna bukatar su rike wayoyin hannu, su shiga shafin koyo na yanar gizo wato e-learning, sannan su shiga sashin ji da gani.
  • Shiga yanar gizo a makarantu ya kai kaso 54%, har yanzu dai muna da sauran aiki.